Shekara daya bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, abokan tafiyarsa a lokacin da yake raye sun shirya wani gagarumin taron tunawa da shi a Abuja babban birnin kasar.
Buhari na daga cikin yan siyasa kalilan wadanda suke da tarin mabiya da masoya a lokacin rayuwarsa, lamarin da ya sanya ya rika samun dimbin kuri’u a duk lokacin da ya yi takara, tun yana faduwa, har zuwa lokacin da ya samu nasarar zama shugaban kasa a shekarar 2015.
A ranar 13 ga watan Yulin 2025 ne tsohon shugaban kasar ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan, shekara biyu bayan sauka daga mulki. Bayan rasuwarsa, ya bar babban gibi, inda aka rika tababar ko za a samu wani da zai gaji farin jininsa da akidar siyasar irin tasa a nan kusa.
Masana siyasa kamar Kabir Sufi sun ce halin da mukarrabannin Muhammadu Buhari suka samu kansu a ciki ya samo asali ne tun kafin saukar gwamnatin marigayin. “Tun gabanin rasuwar tsohon shugaban kasar, a siyasance an samu rarrabuwar kai tsakanin wasu daga cikin manyan na hannun damansa,” in ji Sufi.
Yayin da wasu suka ci gaba da biyayya ga gwamnatin magajinsa Bola Tinubu, wasu sun yi hannun riga da ita, har ma suka rika jayayya da kuma adawa da ita. Sai dai a lokacin Buhari bai taba fitowa fili ya nuna bangaren da ya fi rinjaya ba.
Mutane irin su tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi duk sun barrance wa gwamnatin Tinubu har ma suka sha alwashi kalubalantar ta, tun lokacin Muhammadu Buhari na da rai. Haka lamarin ya ci gaba ko bayan rasuwar tasa.
Wadannan na daga cikin wadanda suka tsinci kansu cikin komar hukumomin bincike kan zargin aikata badakala. Abubakar Malami: Hukumar EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami a kotu kan zargin amfani da mukami ba bisa ka’ida da safarar haramtattun kudade da kuma abubuwan da suka shafi wasu kadarorin da aka mayar wa Najeriya daga kasashen waje. Gabanin haka Abubakar Malami ya kasance cikin jagororin yin hadakar yan hamayya karkashin jam’iyyar ADC, wadanda suka sha alwishin kalubalantar shugaban Najeriya Bola Tinubu a zaben kasar na 2027.
Nasir El-Rufai: A watan Fabarairun 2026 ne hukumomin bincike irin su EFCC da ICPC har da da hukumar tsaro ta farin kaya suka kaddamar da bincike da tuhume-tuhume a kotu kan tsohon gwamnan na jihar Kaduna. Shi ma yana daya daga cikin ginshikan jam’iyyar hadakar yan hamayya ta ADC, kuma ya kasance daya daga cikin wadanda suka fi sukar gwamnatin Bola Tinubu. Daga cikin tuhume-tuhumen da aka masa a kotu akwai karkatar da kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida, da mallakar kadarorin jama’a ba bisa ka’ida ba, da halasta kudaden haram sai kuma wata tuhumar kan zargin shi da satar sauraron wayar mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu.
Akwai kuma wasu daga cikin na kusa da marigayi Muhammadu Buhari wadanda suka raba gari da gwamnatin shugaba Tinubu mai ci, amma ba su shiga hannun hukumomin bincike ba. Irin wadannan sun hada da: Wannan sun kunshi mutanen da suka fada komar hukumomin bincike na Najeriya, mafi yawansu bisa laifin almundahana. Hadi Sirika: Hadi Sirika, shi ne tsohon ministan sufurin jiragen sama. Hukumar EFCC ta gurfanar da Sirika a kotu game da harkallar da ta shafi samar da kamfanin jirgin sama mallakar gwmnatin Najeriya. Hukumar ta zarge shi da yin amfani da ofishinsa wajen yi wa ‘yarsa Fatima da mijinta Jalal Hamma alfarmomi ta hanyar ba su aikin bayar da shawarwari a Nigeria Air, da kuma ba su kwangilar gina wani bangare na filin jirgi a Katsina.
Saleh Mamman: A ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026 ne babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon ministan lantarki a Najeriya, Saleh Mamman shekara 75 a gidan yari kan almundahanar kudi fiye da naira biliyan 33. Kotu ta ce ta samu Saleh da aikata laifuka 12 da hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa – EFCC – ta tuhume shi da su masu alaka da hada baki da almundahana.
Sadiya Faruk: A cikin watan Mayun 2026 ne hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohuwar ministar jinkai ta Najeriya, lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na internet, ta ce tana neman tsohuwar ministar ne bisa zarge-zarge masu alaka da almundahanar kudade.
Akwai kuma wasu na hannun Muhammadu Buhari wadanda suka koma gefe ba tare da ana jin duriyarsu ba, irin wadannan sun hada da: Kusan za a iya cewa da wuya ka ga manyan mukarrabannin marigayi Muhammadu Buhari a cikin gwamnatin Bola Tinubu. Hakan kuwa ya samo asali tun lokacin da tsohon shugaban kasan ke da rai. Sai dai akwai wadanda suka dasa a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari kuma suna damawa a wannan gwamnati ta Bola Tinubu, kamar: Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa a Najeriya ya ce: “Duk da Muhammadu Buhari na da dimbin mabiya da magoya baya, siyasarsa ba ta kafa wasu gungu ba ne ko kuma wata tafiya wadda za ta ci gaba ko da ba ya nan ba”. Ya kara da cewa rarrabuwar mabiyansa ta samo asali ne tun yana raye: “an yi ta zargin ko da a jam’iyyarsa ta APC ya bar kowa ne ya ya yi abin da ya ga dama. “Shi bai yadda a kan cewa akwai wata siyasa ta gidan Buhari ko sai an yi wata tafiya ta Buhari ba,” in ji Kari. “Babu wani abu da za a ce ita ce akida ta zaihiri ta Buhari wadda za a ce za a ci gaba da bin ta. “Ba kamar irin akidar su Malam Aminu Kano ko Awolowo ba, wadanda za a iya cewa ga yan gani-kashe-ninsu. Dama abin aka san shi a kai shi ne, shi mai gaskiya ne, mai son a yi abu daidai ne, to amma ko a lokacin rayuwarsa bai kafa wannan akidar ba, bai dage a kan cewa sai ta ci gaba bayan rayuwarsa ba”. Kari ya ce shi ya sa bayan shudewar Buhari sai akidarsa ta kau.