ABUJA, Nigeria – Shugaba Bola Tinubu ya amince da nada Folashade Adekaiyaoja a matsayin Mataimakin Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Jiha (DSS). Adekaiyaoja, wacce ta fito daga jihar Kogi, ita ce mace ta farko da ta rike wannan mukami a tarihin hukumar.
Babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban kasa, amma wata majiya ta bayyawa TheCable cewa nadin na cikin kokarin shugaban na sake tsara hukumar tsaron ta don inganta ayyukanta. Majiyar, wacce ba ta son a bayyana sunanta saboda ba ta da izinin yin magana kan nadin, ta ce Tinubu yana da niyyar dawo da kwararru a cikin hukumar.
Ta kara da cewa nadin, wanda shi ne na farko da wani shugaban kasa ya yi a tarihin Nigeria, yana da nufin inganta ci gaban aiki ga ma’aikatan hukumar. TheCable ta fahimci cewa Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ya ba da shawarar Adekaiyaoja ta hanyar Oluwatosin Ajayi, Darakta Janar na DSS.
A watan Disamba na 2024, Shugaba Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su gabatar da shirye-shiryen inganta hidimar su, kuma nadin Adekaiyaoja ana ganin wani muhimmin mataki ne a wannan hanyar. Ya kuma yi alkawarin tallafawa DSS da sauran hukumomin tsaro da kayan aikin fasahar zamani na Artificial Intelligence don yaki da rashin tsaro.
Darakta Janar na DSS, Oluwastosin Ajayi, a lokacin da ya karbi mukaminsa a karshen watan Agusta 2024, ya yi alkawarin yin gyare-gyare a cikin hukumar, wanda zai mayar da ita daya daga cikin hukumomin tsaro mafi inganci a duniya.