ABUJA, Najeriya – Sanata Ali Ndume, wanda ya kasance daya daga cikin masu sukar kudirin gyaran dokokin haraji a Najeriya, ya ce ya kamata a ci gaba da jiyo shawarwarin sauran al’umma domin a tsaya kan mataki guda. Ndume ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shafin BBC Hausa.
Sanatan ya ce akwai sauran abubuwan da ya kamata a gyara bayan matsayar da gwamnonin suka cimmawa. “Abinda gwamnoni suka yi ci gaba ne, sai dai kwalliya ba ta gama biyan kudin sabulu ba, don har yanzu bamu san cikakken bayani akan dokokin ba,” in ji Ndume.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya gabatar wa Majalisar Dokokin Tarayya kudurin yin gyaran fuska ga dokar haraji ta kasar, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a kasar. Batun ya kai ga cewa shugaba Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya sun jingine batun muhawara da amincewa da dokar har sai bayan an sake yin nazari a kanta.
A zaman da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja, gwamnonin sun yi gyare-gyare ga kudurin harajin na shugaba Tinubu, musamman bangaren rabon harajin cinikayya na VAT, wanda shi ne ya fi janyo cece-ku-ce. Shawarar da gwamnonin suka cimma na nuna cewa sun rage yawan kudin harajin VAT da za a raba tsakanin jihohi bisa la’akari da gudumawar da kowace jiha ta bayar wurin tara harajin.
Sai dai kuma shawarar gwamnonin ta kara yawan kason kudin a kan yadda yake tun asali. Tun farko, sabon tsarin rabon harajin VAT da ke kunshe a kudurin yin gyara ga dokar haraji da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar dokoki ya bukaci a ware kashi 60 cikin dari ne domin rabawa gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar.
Wanda hakan ya nunka har sau biyu a kan asalin tsarin da ake amfani da shi na kashi 20 cikin dari. Shawarar da gwamnonin suka yanke na nuna cewa an kara kashi 10 cikin dari a kan tsarin da ake amfani da shi a yanzu, yayin da aka zabtare kashi 30 cikin dari daga abin sabon tsarin da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisa.