Paul Onwuanibe, wanda ya kafa kamfanin Landmark Africa Group, ya bayyana irin tasirin da rushewar Landmark Leisure Beach ya yi kan harkokin kasuwanci da rayuwar mutane. A cikin wata hira da ya yi a shirin The KK Show ta YouTube a ranar Lahadi, Onwuanibe ya bayyana cewa rushewar ta yi illa ga zuba jarin sama da dala miliyan 30 kuma ta shafi rayuwar dubban mutane.