LONDON, United Kingdom – Shugaban jam’iyyar Conservative ta Burtaniya, Kemi Badenoch, ta bayyana damuwarta game da illolin gwamnati mara kyau kamar ta Najeriya, inda ta kuma yi kira ga gyara tsarin mulki a Birtaniya don hana irin wadannan sakamako.
Badenoch ta yi maganar ne a ranar Alhamis yayin jawabinta na farko a shekara a wani taron da kungiyar tunani ta Onward ta shirya. Ta yi nuni da bukatar sake fasalin tsarin mulki, inda ta yi karin bayani game da yadda gwamnatin Najeriya ta kasa tafiyar da al’amuran kasar, wanda ya haifar da talauci da rashin tsaro.
“Na san yadda ake rasa abin da kake da shi. Ba na son Birtaniya ta rasa abin da take da shi,” in ji Badenoch. Ta kara da cewa ta girma a wata kasa matalauci kuma ta ga yadda iyalinta suka zama matalauta duk da kokarin da suke yi.
Badenoch, wacce ta girma a Najeriya kafin ta koma Burtaniya tana da shekaru 16, ta bayyana cewa ta yi hijira tare da £100 na karshe da mahaifinta ya bata don neman rayuwa mafi kyau. Ta kara da cewa ba za ta yarda irin wannan halin ya faru a Burtaniya ba.
Wannan ba karo na farko da Badenoch ta yi tir da gwamnatin Najeriya ba. A baya, ta kuma soki ‘yan sandan Najeriya da cewa sun zama ‘yan fashi da ke yiwa al’umma barazana. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya mayar da martani kan kalaman Badenoch, inda ya ce ta canza sunanta idan ba ta son alaka da Najeriya.
Maganganun Badenoch sun zo ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro, wanda ya sa wasu ‘yan Najeriya suka yi hijira zuwa kasashen waje don neman rayuwa mafi kyau.