SHENZHEN, China – Wani dan kasar China da aka samu da laifin kashe wani yaro dan makaranta a Japan a watan Satumba na bara, an yanke masa hukuncin kisa a ranar 24 ga Janairu, 2025. Yaron dan shekara 10 ya rasu ne bayan wani harin wuka da aka kai masa a hanyarsa ta zuwa makaranta a birnin Shenzhen.
Hukuncin ya zo ne kwana guda bayan yankewa wani dan China makamancin wannan hukunci kan kai harin wuka a wata motar makaranta a birnin Suzhou. A lokacin harin, wata mata ‘yar China ta rasa ranta a kokarin kare fasinjoji ‘yan Japan da aka yi kokarin kashewa. Dukkanin laifuka biyu sun girgiza ‘yan Japan mazauna China.
Mahukunta Taliban a Afghanistan sun yi alla-wadai da bukatar sammacin kama shugabanninta, da aka gabatar a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, wanda suke cewa siyasa ce kawai. Ma’aikatar ketaren Taliban ta ce wannan wani shiri ne mara alkibila da adalci a cikinsa.
A jiya Alhamis, babban mai gabatar da kara a Kotun ICC, Karim Khan ya nemi kotu ta bada sammacin kama jagoran Taliban, Haibatullah Akhundzada da babban mai shari’a Abdulkarim Haqqani kan cin zarafi mata, manya da kanana.