Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar da wasu gyare-gyare da ake ganin sun fi amfanar abokan huldarsa da jami’an gwamnati fiye da talakawan Najeriya. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Gbadebo Rhodes-Vivour, dan takarar gwamnan jihar Legas a zaben 2023.
Rhodes-Vivour ya bayyana cewa, duk da cewa gwamnatin Tarayya ta yi iƙirarin cewa gyare-gyaren da ta yi na nufin inganta rayuwar al’umma, amma sakamakon ya nuna cewa abokan huldar shugaban kasa da jami’an gwamnati ne suka fi cin gajiyar su.
A cewarsa, yawancin manufofin da aka gabatar, kamar rage tallafin mai da kuma ƙarin haraji, sun yi tasiri mai tsanani ga talakawa, yayin da masu hannu da shuni ke ci gaba da samun fa’ida ta hanyar hanyoyin da ba a sani ba.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali kan hanyoyin da za ta bi don tabbatar da cewa duk gyare-gyaren da ta yi na nufin amfanar kowa, ba na wasu mutane kaɗan ba.