ABUJA, Nigeria – Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Shafin Rajista na Matasa Manoma, wani shiri na musamman da aka tsara don magance matsalolin rashin aikin yi da talauci a fadin ƙasar. Ministan Ci gaban Matasa, Comrade Ayodele Olawande, ya sanar da ƙaddamar da shirin ne a wani taron da aka gudanar a Abuja.
Shirin, wanda aka haɗa kai da shirin NIYEEDEP (Nigerian Youth Economic Engagement and De-Radicalisation Programme), an tsara shi ne don samar da damar tattalin arziki ga matasa da kuma ƙarfafa aikin noma a ƙasar. Ministan ya bayyana cewa shirin zai samar da ayyukan yi miliyan shida ga matasa a shekarar 2025 a fannoni kamar noma, abinci da abin sha, da masana’antun noma.
“Wannan shiri ba kawai game da ƙara yawan samar da abinci ba ne, amma game da ba da damar matasan Najeriya su sami ƙwarewa mai dorewa, samar da ayyukan yi a yankunan karkara da birane, da kuma tabbatar da jin dadin jama’a da tsaron ƙasa,” in ji Comrade Olawande.
Shafin ya ba wa matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 35 damar shiga shirye-shiryen horar da su kan aikin noma, dabarun noma na zamani, damar samun jagoranci, tallafin kuɗi, da albarkatu don fara ko faɗaɗa ayyukan noma. Ministan ya kuma yi kira ga matasa da su yi amfani da wannan dama don taimakawa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar noma.
Ana iya shiga shafin ta hanyar ziyartar www.niyeedep.org don yin rajista. Wannan shiri ya zo ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar matsalolin rashin abinci da talauci, wanda ya zama barazana ga tsaron ƙasa.