LONDON, Ingila – Majiyoyi sun bayyana cewa, Carney Chukwuemeka na iya barin Chelsea a hukumance a lokacin bazara mai zuwa. Dan wasan tsakiyar, mai shekaru 21, ya koma Borussia Dortmund ta Jamus a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana a watan Janairu, ba tare da wata yarjejeniya ta dindindin ba.
Rahotanni sun nuna cewa, Chukwuemeka na fuskantar kalubale wajen samun gurbin buga wasa a Chelsea a kakar wasa ta bana, inda ya buga wasanni biyar kacal a dukkan gasa. Babu ko daya daga cikin wadannan wasannin da ya buga a gasar Premier League, kuma bai buga cikakken minti 90 ba a ko wanne wasa a kakar wasan bana.
Duk da haka, ya nuna bajintarsa a gasar Premier League a lokacin da ya buga aro a Aston Villa, inda ya buga wasanni 37 a gasar ta Ingila.
Chelsea na da yawan ‘yan wasa a kungiyar, musamman bayan da ta sayi ‘yan wasa da dama a lokacin da Enzo Maresca ke jagoranta. Don haka, ana sa ran kungiyar za ta rage yawan ‘yan wasanta a bazara.
Majiyoyi sun bayyana cewa, ana sa ran Chelsea za ta kasance a cikin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a bazara, don haka, akwai yiwuwar za ta sayar da ‘yan wasan da ke aro a halin yanzu a hukumance.
A halin da ake ciki, Dortmund ta bayyana farin cikinta da dauko Chukwuemeka. Daraktan wasanni na Dortmund, Sebastian Kehl, ya ce: “Carney kwararren dan wasa ne wanda ya taka rawar gani a gasar Premier League tun yana karami. Hazakarsa, da kwazonsa, da kuma jajircewarsa sun sa shi zama dan wasa mai ban sha’awa.”
Ya kara da cewa: “Wannan ci gaban ya dan tsaya a London. Duk da rashin samun gurbi, muna ganin dama mai kyau, kuma muna fatan Carney zai sake samun karfinsa na da.”
A wani ci gaba, Chelsea ta dauko Mathis Amougou a matsayin sabon dan wasan tsakiya. Matashin dan wasan, mai shekaru 19, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru takwas, kuma ana ganinsa a matsayin haziki mai tasowa nan gaba.
Chelsea ta kuma sayar da Cesare Casadei ga Torino a hukumance kan kudi fam miliyan 12.5. Haka kuma, Ipswich Town ta cimma yarjejeniya da Chelsea don siyan Somto Boniface a hukumance.