LONDON, Ingila – Chelsea ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da za su buga gasar cin kofin Turai ta UEFA Europa Conference League, inda ta dawo da Cole Palmer cikin tawagar bayan ya yi jinyar rauni.
Tawagar ta Chelsea, karkashin jagorancin Enzo Maresca, ta samu nasarar lashe matakin rukuni ba tare da Palmer ba, inda ta samu nasara a dukkan wasanni shida da ta buga. Palmer, duk da rashin buga wasa a gasar cin kofin Turai a wannan kakar, shi ne ke kan gaba wajen zura kwallaye a Chelsea da kwallaye 14 a wasanni 24.
Chelsea ta ambaci “kula da gajiya” a matsayin dalilin rashin Palmer a farko, bayan ya taimaka wa Ingila ta kai wasan karshe na Euro 2024 a lokacin bazara. Yanzu dan wasan mai shekaru 22 zai fara buga wasan kwallon kafa a Turai a karon farko a Stamford Bridge.
Baya ga Palmer, an kuma saka Trevoh Chalobah a cikin jerin sunayen ‘yan wasan. Haka kuma, sabon dan wasan da suka saya, Mathis Amougou, mai shekaru 19, wanda ya koma kungiyar daga Saint-Etienne kan yarjejeniyar fam miliyan 12 a ranar karshe ta kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a watan Janairu, shima yana cikin jerin.
Wadannan sauye-sauye na nufin an cire Wesley Fofana da Romeo Lavia daga cikin jerin sunayen. Dukkan ‘yan wasan biyu suna fama da raunuka kuma UEFA ta takaita adadin sauye-sauyen da kungiyoyi za su iya yi a cikin jerin sunayen bayan kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta hunturu zuwa uku kacal.
Maresca ya fahimci cewa Fofana (cikin kwarji) da Lavia (tsoka) za su iya buga wasa sau daya a mako saboda raunin da suka samu.
Axel Disasi, Renato Veiga, Carney Chukwuemeka, Cesare Casadei da Joao Felix duk an cire su daga cikin jerin sunayen ‘yan wasan Chelsea bayan sun samu komawa wasu kungiyoyi a lokacin hunturu.
Chelsea za ta kara da Gent, Real Betis, Copenhagen ko Heidenheim a zagaye na 16. Za a buga wasannin share fage na gasar cin kofin Europa Conference League guda takwas a ranakun 13 ga watan Fabrairu da 20 ga watan Fabrairu. Bayan wasannin share fage, za a buga wasannin zagaye na 16 a ranakun 6 ga watan Maris da 13 ga watan Maris.
Za a buga wasannin quarter-final a ranakun 10 ga watan Afrilu da 17 ga watan Afrilu, wasannin semi-final a ranakun 1 ga Mayu da 8 ga Mayu, sai kuma wasan karshe a Wroclaw a ranar 28 ga Mayu.