MINNA, Niger State – Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana baƙin ciki kan fashewar tankin mai da ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 98 da kuma raunata wasu a jihar Niger. Abin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 2 na rana a hanyar Dikko-Maje Minna da ke Dikko Junction, inda mutane suka yi ta diban mai daga tankin da ya zube, kuma fashewar ta faru.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan inganta hanyoyi don hana irin wannan bala’i. Ya ce, “Wannan bala’i ya ƙara cika jerin abubuwan da suka faru a ƙasarmu saboda rashin ingantaccen tsarin hanyoyi da kuma matsalolin tattalin arziki da suka haifar da wahala ga al’umma tun lokacin da APC ta hau mulki.”
Ologunagba ya kara da cewa, “Yana da ban tausayi cewa ’yan Najeriya, musamman matasa da masu tallafin iyalai, suna ci gaba da mutuwa a kan hanyoyi saboda rashin kulawa da gwamnati. Jam’iyyarmu ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi bincike kan dalilan wannan bala’i da kuma daukar matakan da za su hana faruwar irin wannan abu a nan gaba.”
PDP ta kuma yaba wa jami’an ’yan sanda, masu kashe gobara, Hukumar Kula da Hanyoyi ta Tarayya (FRSC), da sauran jami’an gwamnati da kuma ’yan Najeriya da suka taimaka wajen shawo kan gobarar da kuma ceton wasu wadanda abin ya shafa.
Sanarwar ta kara da cewa, “PDP ta yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, gwamnati da al’ummar jihar Niger. Muna fatan Allah ya ba wa wadanda suka jikkata sauki da kuma ba wa iyalan wadanda suka mutu juriya.”