Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta ba da tayin kwantiragin watanni shida ga dan wasan Dani Olmo, yayin da FC Barcelona ke ci gaba da fuskantar matsalolin rijistar sa. Rahotanni daga Spain sun nuna cewa wakilan Barcelona da Olmo suna tattaunawa kan yarjejeniyar sirri wacce za ta ba shi damar komawa kulob din a lokacin bazara mai zuwa.
Dangane da rahoton Corriere della Sera, tayin da Milan ya yi wa Olmo shi ne zaɓi na ƙarshe don kare shi daga rasa damar buga gasar kwallon kafa. Rashin nasarar rijistar sa a Barcelona na iya shafar damar shiga cikin tawagar ƙasar Spain.
Mashawarcin Olmo ya bayyana cewa dan wasan ya kuduri aniyar ci gaba da zama a Barcelona.