Gwamnatin jihar Borno ta bukaci jama’a su gaggauta tashi daga unguwannin da ambaliyar ta fi muni. Ambaliyar ta malale gidaje da yawa a Maiduguri, lamarin da ya sanya mutane cikin matsala sosai.
Muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa na da muhimmanci a siyasar Amurka. Muhawarar da za a yi tsakanin Donald Trump da Kamala Harris a daren Talata – wanda shi ne karo na farko da za su fafata – zai iya zama zakaran gwajin dafi.
Waɗanda suka ga lamarin sun sheda wa BBC cewa sun ga wasu manya-manyan fashewa a yankin na al-Mawasi jim kaɗan bayan ƙarfe goma sha biyun dare, inda ake iya ganin wuta na tashi sama. Harin Isra'ila ya kashe sama da Falasɗinawa 40 da jikkata gommai.
Ƙasashen Yamma sun zargi Rasha da yi wa EU da Nato kutsen intanet. Hukumomin leƙen asirin Birtaniya da Amurka da wasu ƙasashen Yamma sun yi gargaɗin cewa hukumar leƙen asirin Rasha ce, ke da hannu a jerin kutsen intanet da ake yi wa ƙasashen ƙungiyar tsaro ta Nato da kuma ƙasashen Tarayyar Turai.