Kungiyar Primal Sporting FC ta Abuja ta lashe gasar farko ta Lagos Liga bayan ta doke Applebee FC da ci 9-8 a bugun fanareti a wasan karshe da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena a ranar Juma’a.
Lagos Liga ita ce gasar kwallon kafa ta 7-7 ba ta kwararru ba, wadda aka sanar a watan Mayu kuma ta hada kungiyoyi 16.
Wasan karshe ya gasar ya kasance mai ban mamaki, inda Primal Sporting ta yi nasara bayan wasan ya kare 0-0 a wasan karshe.
An bayar da kyautar N50m ga kungiyar Primal Sporting a matsayin nasarar gasar, wanda ya zama abin farin ciki ga ‘yan wasan kungiyar.