HomePoliticsJinkirin Fara Ayyukan Mulkin Kananan Hukumomi Ya Bata Wa NULGE Rai

Jinkirin Fara Ayyukan Mulkin Kananan Hukumomi Ya Bata Wa NULGE Rai

Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Najeriya (NULGE) ta nuna rashin gamsuwa game da jinkirin fara ayyukan mulkin kananan hukumomi na tsawon watanni shida. Shugaban kungiyar, Comrade Ambali Olatunji, ya bayyana cewa wannan jinkiri ya sanya ma’aikatan kananan hukumomi cikin wahala da damuwa.

Olatunji ya kara da cewa, duk da cewa kotun koli ta yanke hukuncin cewa kananan hukumomi su sami ‘yancin cin gashin kansu, amma ai har yanzu ba a fara aiwatar da hukuncin ba. Wannan ya sanya NULGE ta yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su gaggauta aiwatar da hukuncin kotun.

Ya kuma bayyana cewa, rashin mulkin kananan hukumomi ya haifar da tabarbarewar ayyukan ci gaba a yankunan karkara, inda aka sami karuwar matsalolin tsaro da rashin ingantaccen tsarin samar da ayyukan more rayuwa.

NULGE ta kuma yi kira ga ‘yan majalisar dokokin jihohi da su yi wa al’ummar karkara hidima ta hanyar amincewa da dokar da za ta ba wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu. Hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da kuma samar da ingantaccen tsarin mulki.

RELATED ARTICLES

Most Popular