Gwamnan jihar Bayelsa, Senator Douye Diri, ya roqi kungiyar ma’aikatan ilimi ta jami’o’i (ASUU) ta sashen Jami’ar Niger Delta (NDU) da daina yajin aikin da suka fara a ranar 10 ga Disamba.
Diri ya yi wannan kira ne a wani taro da ya gudana tsakaninsa da shugabannin kungiyar ASUU na jami’ar, inda ya bayyana damuwar sa game da tasirin da yajin aikin ke da shi ga dalibai da al’ummar jihar.
Gwamnan ya ce an yi taro mai mahimmanci tare da shugabannin jami’ar domin samun hanyar magance matsalolin da suka sa kungiyar ta fara yajin aikin.
ASUU ta fara yajin aikin ne saboda wasu matsalolin da suke fuskanta, ciki har da rashin biyan albashi da sauran matsalolin da suke fuskanta a jami’ar.