HomeNewsFasto Adeboye Ya Kira Ga Azumin Kwanaki 100 Domin Neman Zaman Lafiya

Fasto Adeboye Ya Kira Ga Azumin Kwanaki 100 Domin Neman Zaman Lafiya

Babban limamin Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya ayyana azumin kwanaki 100 da addu’a domin neman zaman lafiya da hana barkewar yaƙin duniya na Uku. Yayin taron Holy Ghost Service na farkon shekarar 2025 a Redemption City da ke jihar Ogun, Adeboye ya nuna damuwa kan rikice-rikicen da ke kara yawaita a duniya.

Malamin ya gargadi duniya cewa idan ba a shawo kan waɗannan matsaloli ba, za su iya rikidewa zuwa wani babban rikici mai girman gaske. Ya ce, “Ya kamata mu yi addu’a domin hana sababbin yaƙe-yaƙe da tabbatar da cewa tsoffin rikice-rikice ba za su yi kamari ba.”

Adeboye ya yi bayani kan yadda za a gudanar da azumin, inda ya ce waɗanda suka wuce shekara 70 ba za su cika azumin kamar kowa ba. Ya ce, “Idan kana da shekara 70 zuwa sama, addu’o’inka kawai sun isa zuwa ga ubangiji, ba sai ka yi amfani da azumi wajen aika sakonka ba. Amma idan ka dage kan cewa kana son yin azumin, za ka iya karya azumi da karfe uku na rana. Masu shekara 80 zuwa sama za su karya da karfe 12.”

Malamin ya ce azumin kwanaki 30 na farko zai shafi addu’o’i na neman ci gaban Najeriya, ciki har da yin addu’a kan cin hanci da matsin tattalin arziki. Adeboye ya kara da cewa wasu daga cikin addu’o’in za su kasance masu “zafi,” da nufin shawo kan masu lalata lamuran ƙasar.

Ya gargadi mabiya da su mai da hankali a lokacin azumin, yana cewa, “Idan kana cikin azumi, ka rage magana. Ka tafi coci da karfe 6 na yamma don addu’a tare da mutane.” Adeboye ya yi hasashen cewa wannan shekarar za ta kawo manyan ci gaba da nasarori ga mutane da dama. A cewar malamin, “Ubangiji ya ce ranar da mutane da yawa suke jira za ta zo wannan shekarar. Za a samu dumbin biki da auratayya.”

A matakin duniya, ya yi kira ga addu’o’i domin hana yawaitar bala’o’i irin su ambaliyar ruwa, hadurran gobara da guguwar iska mai tsanani. Ya ja hankali da cewa, “Ubangiji yana son mu yi addu’a don hana waɗannan bala’o’i da kuma sababbin yaƙe-yaƙe. Dole mu tabbatar da cewa tsoffin rikice-rikice ba za su yi kamari ba.”

A wani labarin, shugaban Cocin Freedom Apostolic Revival, Fasto Samuel Adebayo Ojo, ya ce wahalhalun Najeriya za su kare nan da 2025. A wani taron shekara-shekara a Ori Oke Ogo, ya bayyana cewa 2025 za ta zama shekara ta kwanciyar hankali da alheri. Faston ya ce wannan shekarar za ta kawo farfadowa, waraka, da ci gaba, yana kira ga mutane su kasance da kyakkyawan fata da yakini.

RELATED ARTICLES

Most Popular