Yankin tsakiyar Amurka na fuskantar tsananin hunturu tare da saukar dusar ƙanƙara mafi girma cikin shekaru 10, inda yanayin ya jefa miliyoyin mutane cikin fargaba. A jihar Kansas, wata iska mai cike da tsananin sanyi ce ke kaɗawa, yayin da ake hasashen yanayi zai kai maki -29 a ma’aunin salshiyos.
Kamfanin jiragen sama na ‘American Airlines‘ ya fitar da gargaɗi ga filayen jirage kusan 50 a faɗin tsakiyar ƙasar da kuma yankin tekun Atlantika, inda tituna da bishiyoyi suka kasance a cunkushe. Jami’an agaji suna ƙoƙarin share dusar ƙanƙara da ke sauka, yayin da mutane suka yi kira ga jama’a su guji tafiye-tafiye marasa muhimmanci.
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta ce mutumin da ya kai hari a New Orleans a ranar sabuwar shekara, inda ya kashe mutane 14, ya ziyarci birnin har sau biyu kafin ya ƙaddamar da harin. Shamsud-Din Jabbar, wanda aka kashe bayan harin, ya naɗi bidiyoyin wurin da ya kutsa da babbar motar cikin dandalin jama’a. Jami’an sun ce maharin ya shirya harin shi kaɗai kuma yana bincike game da tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen Canada da Masar.