Tsohon Gwamnan Jihar Niger, Babangida Aliyu, ya zargi wadanda suke adawa da kudirin gyaran haraji, inda ya ce suna kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin ƙasar.
Aliyu, wanda ya taba zama shugaban kwamitin gwamnonin arewacin Najeriya, ya bayyana ra’ayinsa a wata sanarwa ta hukuma, inda ya ce wadanda suke adawa da kudirin haraji ba su da ilimi kan harkokin tattalin arziĆ™i.
Ya ce gwamnatin tarayya ta yi kuskure wajen yadda ta gabatar da kudirin haraji, wanda hakan ya sa wasu jahohi suka nuna adawa.
Aliyu ya kuma nuna cewa jahohin arewacin Najeriya, musamman Arewa ta Yamma da Arewa ta Gabas, suna nuna adawa ga kudirin haraji saboda tsoron asarar kudaden shiga da suke samu daga gwamnatin tarayya.