LAGOS, Nigeria – A cikin shekarar 2024, ALX Nigeria ta samar da horo ga fiye da matasa 76,000 a duk fadin kasar, inda ta ba su basira masu muhimmanci a fannonin Fasahar Watsa Labarai, Gudanar da Cloud, Kimiyyar Bayanai, da Taimakon Virtual, da sauransu.
Wannan nasarar ta samu ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin ALX da sama da abokan hulda 30 na gwamnati da masu zaman kansu, ciki har da Wema Bank, 9mobile, SMEDAN, Shecluded, LSETF, da UNDP.
Manajan Janar na ALX Nigeria, Ruby Igwe, ta bayyana cewa burin ALX shi ne samar da damar aiki ga matasa miliyan biyu nan da shekara ta 2030. Ta kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su shiga cikin wannan yunƙuri don taimakawa wajen cimma burin.
ALX ta gayyaci Æ™ungiyoyi masu zaman kansu, gwamnatoci, da kuma mutane É—aya É—aya don su shiga cikin wannan shiri na horar da matasa. Ta kuma yi kira ga masu sha’awar su tuntubi ALX Nigeria ta hanyar sadarwar zamantakewa don fara haÉ—in gwiwa.