Abbie Stockard, wacce ta wakilci jihar Alabama, ta lashe gasar Miss America 2025 a ranar Lahadi, inda ta doke ‘yan takara 51 daga jihohin Amurka, gami da Washington D.C. da Puerto Rico. Gasar dai ta gudana ne a gidan wasan kwaikwayo na Walt Disney a Orlando, Florida.
Stockard, mai shekaru 22, dalibar jinya a Jami’ar Auburn kuma ‘yar wasan cheerleader, ta samu nasarar lashe gasar bayan ta fafata a sassa daban-daban kamar su rigar maraice, fasaha, da kuma fitness. Ta kuma yi rawa a matsayin nuna fasaharta a wakar Lauren Daigle mai suna