Hukumar Yanayi ta China ta bayyana cewa shekarar 2024 ita ce mafi zafi a tarihi, tare da nuna alamun sauyin yanayi da ke haifar da matsaloli masu yawa a duniya.
A cewar hukumar, yanayin zafi ya karu da kashi 1.5 digiri Celsius sama da matsakaicin yanayin da aka samu a zamanin masana’antu, wanda ke nuna cewa sauyin yanayi ya kai matsayi mai tsanani.
Wannan rahoton ya zo ne bayan bincike da yawa da kuma bayanai daga masana kimiyya da hukimomin yanayi na duniya, waÉ—anda suka nuna cewa shekaru masu zafi sun zama ruwan dare a cikin ‘yan shekarun nan.
Hukumar ta China ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙara ƙoƙarin rage hayakin da ke haifar da dumamar yanayi, tare da ba da shawarar amfani da makamashi mai sabuntawa da kuma ingantaccen tsarin noma.