‘Yan ta’adda sun kashe mutum 11, sun kona gidaje da dama a Katsina

0
1

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne, wadanda aka fi sani da ‘yan bindiga, sun kashe mutane 11 tare da raunata wasu da dama a hare-haren da suka kai kan wasu al’ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, wanda ya tabbatar da kashe-kashen da kone-kone, ya ce wasu mutane 13 sun samu raunuka.

“A jiya 9/11/2021 da misalin karfe 1915, ‘yan bindiga a adadinsu, suna harbe-harbe da bindigogi kirar AK 47, sun kai hari a unguwar Katoge da Yanturaku na karamar hukumar Batsari, inda suka kashe 11 tare da raunata mutane 13.

“Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Katsina, ya tura mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, tare da karin rukunin jami’an PMF zuwa yankin domin karfafa tsaro da dawo da kwarin gwiwa ga al’ummomin da abin ya shafa.”

Sai dai majiyoyi daga cikin al’ummar sun ce ‘yan ta’addar sun kashe mutane kusan 13 tare da kona gidaje da motoci da dama yayin harin.

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=27309