Labarai
‘Yan sandan Najeriya sun la’anci “Portable” da kuma shirin gurfanar da shi gaban kuliya
Rundunar ‘yan sanda ta zargi fitaccen mawakin nan da tada hankali da rashin da’a Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi Allah-wadai da abin da wani Habeeb Okikiola da aka fi sani da ‘Portable’ ya aikata a wani faifan bidiyo.
Rundunar ‘yan sandan ta yi ikirarin cewa mawakin ya yi rashin hankali tare da cin mutuncin jami’an da ke aikinsu kawai, matakin da ya dace a hukunta shi a karkashin dokokin Najeriya.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan kasa, CSP Muyiwa Adejobi, ya fitar, ya ce, matakin da mawakin ya dauka na iya haifar da rashin zaman lafiya, har ma da tayar da hankali ga jami’an da ke aiwatar da umarnin kama shi bisa zargin aikata laifuka da dama.
“Hukumar NPF za ta dauki dukkan matakan da suka dace don bincikar abin da ya aikata tare da tabbatar da cewa an gurfanar da shi a gaban kuliya kan duk wani laifin da ya aikata dangane da girman laifin,” in ji Adejobi.
“Rundunar ‘yan sanda ba za ta amince da duk wani aiki na rashin da’a, hari ko kai wa jami’anta da ke bakin aiki ba. Muna bukatar mu mutunta jami’anmu na tilasta bin doka da ke daukar kasadar kiyaye doka da oda da kuma yaki da laifuffuka da aikata laifuka a cikin al’ummarmu.”