Connect with us

Duniya

‘Yan sanda sun mamaye gidan Seun Kuti, sun kwace wayar matar –

Published

on

  A ranar Talata ne rundunar yan sandan jihar Legas ta mamaye gidan fitaccen mawakin nan Seun Kuti domin neman shaidar da za ta sanya shi da wani laifi na daban Jami an tsaron da suka gudanar da binciken sun bayyana cewa sun kwace wayar matar Kuti a yayin samamen Hakan na zuwa ne sa o i bayan da kotun Majistare ta Yaba a ranar Talata ta bayar da belin Seun Sai dai a wani sabon lamari wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya dauki hoton lokacin da jami an yan sanda suka gudanar da bincike a gidan mawakin da ke Akin Osiyemi kusa da Allen Avenue Ikeja Legas Idan dai za a iya tunawa babban sufeton yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ne ya bayar da umarnin a kamo Kuti bayan da ya mari wani dan sanda a kan gadar 3rd Mainland a makon jiya Credit https dailynigerian com police invade seun kuti house
‘Yan sanda sun mamaye gidan Seun Kuti, sun kwace wayar matar –

A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta mamaye gidan fitaccen mawakin nan Seun Kuti, domin neman shaidar da za ta sanya shi da wani laifi na daban.

Jami’an tsaron da suka gudanar da binciken sun bayyana cewa sun kwace wayar matar Kuti a yayin samamen.

Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan da kotun Majistare ta Yaba a ranar Talata ta bayar da belin Seun.

Sai dai a wani sabon lamari, wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya dauki hoton lokacin da jami’an ‘yan sanda suka gudanar da bincike a gidan mawakin da ke Akin Osiyemi, kusa da Allen Avenue, Ikeja, Legas.

Idan dai za a iya tunawa, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ne ya bayar da umarnin a kamo Kuti bayan da ya mari wani dan sanda a kan gadar 3rd Mainland a makon jiya.

Credit: https://dailynigerian.com/police-invade-seun-kuti-house/