Duniya
‘Yan sanda sun karyata rade-radin harin da aka kai gidan shugaban INEC a Bauchi –
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bauchi, ta yi watsi da rade-radin da ke fitowa daga wasu faifan bidiyo cewa wasu ‘yan daba ne suka kai wa gidan Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC hari a Bauchi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil, kuma aka rabawa manema labarai ranar Asabar a Bauchi.
Ya kara da cewa an jawo hankalin hukumar ne kan wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa a kafafen yada labarai cewa an kai hari gidan shugaban INEC na Bauchi.
“Muna matukar son bayyana cewa bidiyon da abin da ke cikinsa gaba daya na bogi ne, domin ba a samu irin wannan taron ba a cikin ko kusa da birnin Bauchi a safiyar yau,” in ji shi.
Mista Wakil ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Aminu Alhassan, ya san illar da bata gari ke haifarwa ga zaman lafiya da tsaro.
“Duk da haka, mun riga mun ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi don gano asalin bidiyon, da nufin tabbatar da cewa wanda ya kirkiro faifan bidiyo ya fuskanci fushin doka.
“Rundunar ‘yan sandan ta nanata cewa babu wani hari da aka kai gidan shugaban INEC a Bauchi,” inji shi.
Kakakin, ya kuma bukaci jama’a da kada su firgita, tare da yin watsi da faifan bidiyon na bogi da kuma abubuwan da ke cikin sa.
NAN
Credit: https://dailynigerian.com/police-dispel-rumours-attack/