Connect with us

Duniya

‘Yan sanda sun kama mutane 40 da laifin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben Zamfara

Published

on

  Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane 40 da ake zargi da aikata barna da sata bayan fitar da sakamakon zaben gwamnan jihar Zamfara a ranar Talata Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami in hulda da jama a na rundunar yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau ranar Juma a A cewarsa wadanda aka kama sun yi amfani da damar sanar da sakamakon zaben gwamna inda suka kai farmaki gidaje da ofisoshin shugabannin jam iyyar APC da kuma cibiyoyin gwamnati Kwamishanan yan sandan jihar Mista Kolo Yusuf wanda ya jagoranci yan sandan hadin gwiwa da sauran jami an tsaro ya shawo kan lamarin daga nan kuma ya kama mutane 26 da ake zargi da hannu a lamarin Haka zalika kwamandojin yankin da DPO sun fara gudanar da irin wannan atisayen a sassan da suke aiki domin kaucewa ta addanci Binciken da jami an yan sanda ke ci gaba da yi ya kai ga kama wasu mutane 14 da ake zargi tare da kwato kadarori da aka sace da kuma barnata in ji shi Ya ce yan sandan na kan bin sawun wasu yan ta adda da suka shiga cikin rikicin Kakakin ya ce CP din ya ba da tabbacin gudanar da bincike mai zurfi da nufin kamo wadanda ake zargi da su gudu da wadanda ake tuhuma domin gurfanar da su a gaban kuliya tare da kwato dukiyoyin da aka sace NAN Credit https dailynigerian com police arrest post election
‘Yan sanda sun kama mutane 40 da laifin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane 40 da ake zargi da aikata barna da sata bayan fitar da sakamakon zaben gwamnan jihar Zamfara a ranar Talata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau ranar Juma’a.

A cewarsa, wadanda aka kama sun yi amfani da damar sanar da sakamakon zaben gwamna, inda suka kai farmaki gidaje da ofisoshin shugabannin jam’iyyar APC, da kuma cibiyoyin gwamnati.

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar, Mista Kolo Yusuf, wanda ya jagoranci ‘yan sandan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro, ya shawo kan lamarin, daga nan kuma ya kama mutane 26 da ake zargi da hannu a lamarin.

“Haka zalika kwamandojin yankin da DPO sun fara gudanar da irin wannan atisayen a sassan da suke aiki domin kaucewa ta’addanci.

“Binciken da jami’an ‘yan sanda ke ci gaba da yi ya kai ga kama wasu mutane 14 da ake zargi tare da kwato kadarori da aka sace da kuma barnata,” in ji shi.

Ya ce ‘yan sandan na kan bin sawun wasu ‘yan ta’adda da suka shiga cikin rikicin.

Kakakin ya ce, CP din ya ba da tabbacin gudanar da bincike mai zurfi da nufin kamo wadanda ake zargi da su gudu da wadanda ake tuhuma domin gurfanar da su a gaban kuliya, tare da kwato dukiyoyin da aka sace.

NAN

Credit: https://dailynigerian.com/police-arrest-post-election/