Connect with us

Kanun Labarai

‘Yan sanda sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Published

on

 Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 42 a dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami in hulda da jama a na rundunar yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau ranar Alhamis hellip
‘Yan sanda sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

NNN HAUSA: Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 42 a dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau ranar Alhamis.

Mista Shehu ya ce an samu nasarar kubutar da wadanda harin ya rutsa da su ne a wani samame da jami’an leken asiri suka gudanar a dajin a ranar Talata.

Ya ce rundunar ‘yan sanda ta gudanar da aikin tare da goyon bayan wasu mutane da ke hada kai da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a jihar.

“Rundunar ‘yan sandan ta dauki matakin ne bisa sahihan bayanan sirri inda suka kai farmaki kan maboyar ‘yan bindigar, inda suka ceto mutane 14 da suka hada da jarirai biyu ‘yan shekara daya kowanne.

“Wadanda abin ya shafa sun sanar da ‘yan sanda cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyukan Nasarawar-Wanke da Rijiya a karamar hukumar Gusau inda suka yi garkuwa da su har tsawon kwanaki 42 a hannunsu,” inji shi.

Malam Shehu ya kara da cewa an mika mutanen 14 ga ‘yan uwansu.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Ayuba Elkanah ya yaba da irin goyon bayan da gwamnati da jama’a ke baiwa ‘yan sanda a kokarin dawo da zaman lafiya a jihar.

NAN

dw h

NNN is a Nigerian online news portal that publishes breaking news in Nigeria, and across the world. We are honest, fair, accurate, thorough and courageous in gathering, reporting and interpreting news in the best interest of the public, because truth is the cornerstone of journalism and we strive diligently to ascertain the truth in every news report. Contact: editor @ nnn.ng. Disclaimer.