Labarai
‘Yan bindiga sun bude wuta kan ‘yan sanda; kashe, sun jikkata da dama a Kogi
A ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka yi wa tawagar ‘yan sanda kwanton bauna, inda suka kashe biyu tare da raunata wasu jami’ai biyu a Kogi.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, William Ovye-Aya ya fitar, ya ce an kai harin ne kan tawagar ‘yan sandan a kan hanyar Agbaja, Lokoja, inda ‘yan ta’addan suka fito daga daji suka far wa tawagar bayan sun isa sintiri na yau da kullum.
“Abin takaici da bakin ciki, rundunar ta rasa jami’anta guda biyu.
“Duk da haka, ‘yan bindigar sun gudu kafin tawagar jami’an tsaro ta isa wurin da lamarin ya faru,” in ji shi.
Mista Ovye-Aya ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Akeem Yusuf, ya tura tawagar ‘yan sanda zuwa yankin domin bin diddigin ‘yan bindigar domin kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
A cewar sa, CP ya kuma umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, bincike, da ya fara gudanar da bincike a kan wannan mumunan lamari.
Mista Ovye-Aya ya ce kwamishinan ya yi kira ga al’ummar yankin da su taimaka wa ‘yan sanda da sahihan bayanai kan ko su wanene ‘yan ta’addan domin baiwa rundunar damar bincikar laifukan da suka aikata.
(IN)