Wasu ‘yan bindiga sun kashe fararen hula 10 a wani harin da aka kai Burkina Faso

0
3

Akalla fararen hula 10 ne wasu ‘yan bindiga suka kashe tare da sace wasu hudu a ranar Litinin a kauyen Dambam na kasar Burkina Faso, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AIB ya ruwaito a ranar Talata.

A cewar AIB, wani harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai kan al’ummar garin Dambam da ke yankin Markoye mai tazarar kilomita 16 daga kan iyaka da Nijar.

AIB ta kuma ruwaito cewa, dakarun kasar Burkina Faso sun kai wani samame cikin gaggawa a yankin.

Galibi mutanen garin Dambam suna zuwa kasuwar Markoye duk ranar litinin da kafa, babura uku ko kuma na dabbobi domin sayar da shanunsu.

Xinhua/NAN

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=26751