Duniya
Wani mutum ya yi garkuwa da mahaifinsa, ya karbi kudin fansa Naira miliyan 2.5 —
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara da ke yaki da masu garkuwa da mutane ta cafke Issa Naigheti da laifin yin garkuwa da mahaifinsa, Bature Naigboho tare da karbar kudin fansa naira miliyan 2.5.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ajayi Okasanmi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Ilorin.
Mista Okasanmi, Sufeto na ‘yan sanda, ya ce jami’an ‘yan sanda sun kama Naigheti a ranar 4 ga watan Janairu a kewayen unguwar Kambi, Ilorin, a yayin da ake bin sahun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
“Ya amsa a lokacin da ake masa tambayoyi cewa ya hada baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo, kuma ya karbi Naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansa.
“Ana ci gaba da kokarin kama sauran wadanda suka yi masa laifi, kuma za a mika karar zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin,” in ji Mista Okasanmi.