Connect with us

Kanun Labarai

Syria ta ce harin da Isra’ila ta kai a lardin Homs ya kashe soja daya

Published

on

Kafafen yada labarai na Syria sun rawaito cewa wani sojan Siriya ya rasa ransa yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai a tsakiyar lardin Homs.

Tashar talabijin ta Syria da kamfanin dillancin labarai na Syria, SANA, sun ce jim kadan bayan tsakar dare Isra’ila ta kai hari a gabashin garin Homs, inda ta nufi hasumiyar sadarwa da wuraren da ke kewaye.

A cewar rahoton, harin ya yi sanadiyar mutuwar soja daya da raunata wasu uku, ya kara da cewa gine -ginen sun kuma samu barna.

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin dan adam ta Siriya da ke Burtaniya, wacce ke sa ido kan tashe-tashen hankula a kasar da yaki ya daidaita, ta ba da wani labari na daban daga kafafen yada labaran gwamnatin Syria.

Sanarwar ta ce an kashe akalla mayakan sa-kai hudu masu goyon bayan Iran yayin da wasu 7 suka jikkata a hare-haren na Isra’ila.

Kungiyar da ke sa ido ta ce wadanda suka mutu dukkansu ‘yan kasar Siriya ne da ke aiki da mayakan Iran da kuma kungiyar Shi’a ta Lebanon Hezbollah.

“Ba mu yin tsokaci kan rahotannin da ke fitowa daga kafafen yada labarai na kasashen waje,” in ji wani kakakin sojin Isra’ila.

Ana ganin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Siriya a matsayin wani yunkuri na hana Iran, daya daga cikin manyan kawayen Shugaba Bashar al-Assad ta gina tasirin sojinta a yankin.

dpa/NAN