Labarai
Sule ya jajantawa NNPP bisa rasuwar magoya bayansa
Sule ya jajantawa jam’iyyar NNPP bisa rasuwar magoya bayan Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata ya jajantawa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) bisa rasuwar magoya bayanta a wani hatsari.
Wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP sun mutu a wani hatsari a ranar Asabar bayan wani gangamin maraba da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Rabi’u Musa-Kwankwaso zuwa jihar.
Sakon yana kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Ibrahim Adra, babban sakataren yada labarai na gwamnan kuma ya mika wa manema labarai ranar Litinin a Lafiya.
Adra, a cikin sanarwar, ya ce gwamnan ya nuna alhininsa game da hatsarin.
“Gwamnan ya bayyana asarar rayukan ‘yan kasa a irin wannan yanayi a matsayin abin bakin ciki kuma ya bukaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su yi taka-tsan-tsan a kowane lokaci,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya jajantawa iyalai da abokanan wadanda suka rasu da kuma shugabannin jam’iyyar.