Duniya
Shugaban ‘yan kabilar Igbo da ya yi barazanar gayyatar IPOB zuwa Legas a hannun SSS – ‘Yan sanda —
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta tabbatar da cafke Frederick Nwajagu, Eze Igbo na Estate Ajao a jihar Legas.
Da yake tabbatar da kamun, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce an kai Mista Nwajagu a hannun hukumar tsaro ta farin kaya, SSS.
An tattaro cewa rundunar hadin guiwa ta ‘yan sanda da jami’an SSS sun kama shugaban na Igbo a ranar Asabar a lokacin wani samame da tsakar dare.
Kama shi ya biyo bayan barazanar gayyatar mambobin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB domin su kwato dukiyoyin ‘yan kabilar Igbo a jihar.
Da yake magana a wani faifan bidiyo a ranar Juma’a, Mista Nwajagu ya ce, “Dole ne mu samu tsaron mu domin su daina kai mana hari da tsakar dare, da safe da kuma da rana.
“Lokacin da suka gano cewa muna da tsaron mu, za su yi tunani sosai kafin su kai mana hari. Ba zan ce ko kalma daya da za a boye ba.”
Kakakin ‘yan sandan ya ce, “An kai harin ne da tsakar dare. Jami’an tsaron ba su same shi a fadarsa ba. Amma mun gano ta hanyar tattara bayanan sirri cewa ya sauka a wani otal da ke Ejigbo.
“An gano shi a inda aka kama shi da misalin karfe 1 na safe.
“Yanzu haka yana hannun DSS, inda ake bincike a kansa.”
Credit: https://dailynigerian.com/arrested-igbo-leader/