Kanun Labarai
Shugaban riko na Sri Lanka ya ayyana dokar ta-baci, dokar hana fita –
Mukaddashin shugaban kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe a ranar Laraba ya ayyana dokar ta baci tare da sanya dokar hana fita domin shawo kan wata sabuwar zanga-zanga a Colombo.
Wickremesinghe, a cikin wani faifan bidiyo da aka watsa a talabijin ya ce an ba da umarnin ne biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna cewa masu zanga-zangar sun mamaye majalisar dokokin kasar, da ofishin Firayim Minista da kuma gidajen kwamandojin hidima.
An rantsar da Wickremesinghe a matsayin shugaban rikon kwarya bayan Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar zuwa Maldives da safiyar yau bayan zanga-zangar.
Wickremesinghe ya kasance Firayim Minista.
Bayanin nasa ya zo ne yayin da sama da mutane 3,000 yawancinsu daliban jami’a ke ci gaba da zanga-zanga a kusa da ofishin firaministan inda wasu daga cikinsu suka mamaye ginin.
Sai dai an jibge dakaru masu yawa a kewayen yankin inda suke kokarin korar masu zanga-zangar ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye.
dpa/NAN