Sani Buhari Daura, ‘maginin’ Ship House, ya rasu yana da shekaru 90

0
15

Shahararren dan masana’antar Kano Sani Buhari Daura ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.

Dan sa Abdulrasheed Daura ya tabbatar wa DAILY NIGERIAN rasuwar, inda ya ce mahaifinsa ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a birnin Dubai.

Marigayi Daura ya kasance shugaba kuma ya kafa kamfanoni da dama irin su Bayajidda Nigerian Limited, Standard Construction Limited, Buhari Properties and Development Company da Katsina Oil Mill.

Kamfaninsa, Standard Construction Limited, ya gina daya daga cikin fitattun gine-gine a Abuja, watau Ship House, wanda a yanzu ma’aikatar tsaro ta mamaye.

Kamfanin ya kuma gina ofisoshin bankin NEXIM da bankin Lion a Abuja, da dai sauran hanyoyi da asibitoci da makarantu.

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=28469