Kanun Labarai
Ronaldo ba ya cikin tawagar Manchester United bayan wani bala’i –
Cristiano Ronaldo ba zai buga karawar da Manchester United za ta yi da Liverpool a gasar Premier ranar Talata a Anfield, sakamakon rasuwar dansa da aka haifa.
Dan wasan ya sanar da wannan labari mai ban tausayi a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, wanda ya haifar da dimbin sakonnin goyon baya daga sassan duniya na kwallon kafa da sauran su.
United ta tabbatar da rashin Ronaldo a shafinta na yanar gizo, inda ta ce: “Iyali ya fi komai muhimmanci kuma Ronaldo yana goyon bayan masoyansa a wannan lokaci mai matukar wahala.
“Saboda haka, za mu iya tabbatar da cewa ba zai buga wasan da za su yi da Liverpool a Anfield ranar Talata da yamma ba, kuma muna jaddada bukatar sirrin dangi.
“Cristiano, duk muna tunanin ku kuma muna aika ƙarfi ga dangi.”
dpa/NAN