Rashin tsaro: Buhari ya gana da shugabannin Igbo a Aso Villa

0
9

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a Abuja ya gana da wasu shugabannin Igbo karkashin jagorancin Mbazulike Amaechi a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja.

Shugabannin kabilar Igbo da suka halarci taron sun hada da Bishop Sunday Onuoha, tsohon gwamna Chukwuemeka Ezeife, Tagbo Amaechi da kuma Cif Goddy Uwazurike.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, suma sun halarci taron.

NAN ta ruwaito cewa ajandar taron da ya kwashe bai wuce sa’a daya ba bai bayyana ga manema labarai ba.

Mahalarta taron dai ba su yi magana da manema labarai kan sakamakon ganawarsu da shugaban kasar ba.

Sai dai NAN, ta tattaro daga majiya mai tushe cewa mai yiwuwa taron ya tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi kasa da suka hada da tsaro da cigaban tattalin arziki a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar nan.

NAN

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=27954