Labarai
Ranar Kasa ta Uganda
Ranar kasa ta Uganda A madadin Amurka, ina taya al’ummar Uganda murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai da kuma irin ci gaban da kasar ta samu tun daga wancan lokaci.
Shekaru da dama, jama’ar Amurka da Uganda sun ba da hadin kai don amfanin kasashen biyu, musamman a fannin kiwon lafiyar duniya da na jama’a.
Muna kuma godiya da irin rawar da Uganda ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, ta hanyar taka rawar gani a ayyukan wanzar da zaman lafiya da manufofin karbar ‘yan gudun hijira.
Amurka na fatan samun karin shekaru masu yawa na hadin gwiwar moriyar juna da Uganda.