Ortom ya yabawa Buhari kan bashin N18bn da ya baiwa jihohi

0
14

Gwamna Samuel Ortom na Benue ya yabawa gwamnatin tarayya kan sakin Naira biliyan 18 daga babban bankin Najeriya domin tallafawa gwamnatocin jihohi.

Mista Ortom ya yi wannan yabon ne a ranar Juma’a a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin Benue, Makurdi.

Gwamnan wanda ya fayyace cewa kudaden ba tallafi ba ne, rance ne, ya ce za su taimaka wa galibin jihohin wajen tunkarar wasu muhimman kalubale na ci gaba.

Mista Ortom ya ce nan ba da jimawa ba majalisar zartarwa ta Benue, EXCO, za ta yi taro domin ba da fifiko wajen amfani da kudaden.

Ya bayyana cewa ga jihar da ta yi fama da gibin kasafin kudin, kudaden za su tallafa a muhimman fannoni kamar biyan basussukan albashi da kuma magance matsalar karancin ababen more rayuwa.

“Za mu tabbatar da cewa yin amfani da kudin ya yi tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar mu,” ya tabbatar.

Mista Ortom ya yi nadamar kashe wani limamin coci da aka yi kwanan nan a kauyen Tor Donga da ke karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar, ya kuma ba da tabbacin cewa za a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro a jihar domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

NAN

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=27958