Connect with us

Labarai

Mutane 15 ne suka mutu a arewacin Indiya sakamakon ambaliyar ruwan damina

Published

on

 Mutane 15 ne suka mutu a arewacin Indiya bayan damina ta kashe akalla mutane 15 a Indiya bayan da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a kusa da tsaunin Himalayan kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Asabar Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sun zama ruwan dare kuma suna haifar da barna a lokacin damina ta Indiya Masana sun ce sauyin yanayi na kara yawan munanan yanayi a duniya tare da lalata dazuzzuka da sare itatuwa da ayyukan raya kasa a Indiya wanda ke kara ta azzara rayukan mutane Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce an garzaya da jami an ceto zuwa gundumar Mandi da ke jihar Himachal Pradesh da ke arewacin kasar inda ambaliyar ruwan ta lakume gidaje biyu tare da kashe mutane takwas Sanarwar ta kara da cewa zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane bakwai a fadin jihar Hotunan labaran talabijin sun nuna wani bangare na gadar jirgin kasa da ruwan ya tafi da shi a gundumar Kangra da ke kusa A gundumar Hamipur ambaliyar ruwa ta makalewa mutane 19 a saman rufin gine ginen yankin kafin jami an agajin gaggawa su ceto su An rufe makarantu a gundumomin da abin ya fi shafa Himachal Pradesh mai kyan gani ya shahara saboda tsaunukan da ke cike da dusar an ara kuma ya shahara da masu yawon bu e ido A watan da ya gabata mutane takwas ne suka mutu bayan ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a wani sansanin mahajjata a yankin Kashmir da ke kusa Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya afkawa yankin arewa maso gabashin Indiya a cikin watan Yuni inda kusan mutane 40 suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta mamaye wani sansanin da ke dauke da ma aikatan layin dogo da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya a jihar Manipur
Mutane 15 ne suka mutu a arewacin Indiya sakamakon ambaliyar ruwan damina

Mutane 15 ne suka mutu a arewacin Indiya bayan damina ta kashe akalla mutane 15 a Indiya bayan da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a kusa da tsaunin Himalayan, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Asabar.

Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sun zama ruwan dare kuma suna haifar da barna a lokacin damina ta Indiya.

Masana sun ce sauyin yanayi na kara yawan munanan yanayi a duniya, tare da lalata dazuzzuka da sare itatuwa da ayyukan raya kasa a Indiya wanda ke kara ta’azzara rayukan mutane.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce, an garzaya da jami’an ceto zuwa gundumar Mandi da ke jihar Himachal Pradesh da ke arewacin kasar inda ambaliyar ruwan ta lakume gidaje biyu tare da kashe mutane takwas.

Sanarwar ta kara da cewa zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane bakwai a fadin jihar.

Hotunan labaran talabijin sun nuna wani bangare na gadar jirgin kasa da ruwan ya tafi da shi a gundumar Kangra da ke kusa.

A gundumar Hamipur, ambaliyar ruwa ta makalewa mutane 19 a saman rufin gine-ginen yankin, kafin jami’an agajin gaggawa su ceto su.

An rufe makarantu a gundumomin da abin ya fi shafa.

Himachal Pradesh mai kyan gani ya shahara saboda tsaunukan da ke cike da dusar ƙanƙara kuma ya shahara da masu yawon buɗe ido.

A watan da ya gabata, mutane takwas ne suka mutu bayan ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a wani sansanin mahajjata a yankin Kashmir da ke kusa.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya afkawa yankin arewa maso gabashin Indiya a cikin watan Yuni, inda kusan mutane 40 suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta mamaye wani sansanin da ke dauke da ma’aikatan layin dogo da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya a jihar Manipur.