Kanun Labarai
Muna shirya wani shiri a boye kan wadanda suka saki bidiyon dala na – Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sha alwashin yin maganin wadanda suka fitar da bidiyon shi yana cusa daloli a cikin manyan aljihunsa, yana mai jaddada cewa ba zai tona asirin tsare-tsaren da yake yi ba.
Gwamnan yayi magana ne a wani shirin BBC Hausa, A Fada A Cika, wanda aka gabatar a yammacin Juma’a.
Ku tuna cewa jaridar DAILY NIGERIAN a ranar 15 ga Oktoba, 2018 ta buga wasu faya-fayan bidiyo na musamman wanda ke nuna gwamnan yana karbar kudi daga wani dan kwangila.
“Babu shakka bidiyon karya ne,” in ji gwamnan, ya kara da cewa “muna yin wasu tsare-tsaren karkashin kasa, wanda ba za mu bayyana su ba. Amma ina tabbatar muku karya ne, kuma duk wadanda suke bayansa za su ji kunya. ”
Lokacin da mai tambayan ya sake maimaita tambayar, yana neman ya sani ko gwamnan ne a cikin faya-fayen bidiyon, Mista Ganduje ya ce an shirya faifan bidiyon ne don a nuna shi yana tattara wani abu.
“Hatta hotonka ana iya batawa don nuna wani abu a kai ko hannunka. Kuma ka san abu ne mai yiyuwa. Mutane koyaushe sukan yarda da ƙarya.
“Gaskiyar ita ce, za mu dauki mataki a kan lamarin,” in ji gwamnan, abin da ya haifar da tambaya a kan ko wani irin yanayi ya faru.
“Karya ne. Babu wani abu irin wannan da ya taɓa faruwa. Yana daga cikin makircin da zai hana ni tsayawa takarar – kuma na tsaya takara; don dakatar da ni daga cin zabe – kuma na ci. Amma wannan ba batun ba ne, babban batun da za mu magance wadanda ke bayan sa, ”inji shi.
A ranar 15 ga Nuwamba, 2018 gwamnan ya ja jaridar DAILY NIGERIAN da mawallafinta, Jaafar Jaafar kan shirye-shiryen bidiyo da kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa wanda ke nuna gwamnan yana karbar cin hanci da rashawa cikin kudin da yawa daga hannun ‘yan kwangila.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa karar da aka shigar a wata babbar kotun jihar, na zuwa ne wata daya bayan wallafa labarin bidiyo na karbar rashawa.
A karar da lauyan Gwamna Ganduje, Nuraddeen Ayagi ya shigar, gwamnan yana neman kotun da sauran su ta hana jaridar DAILY NIGERIAN ci gaba da wallafa abin da ya kira “shirye-shiryen bidiyo na batanci.”
Gwamnan ya kuma bukaci kotu ta umarci DAILY NIGERIAN da ta biya jimlar Naira biliyan 3 a matsayin diyya saboda bata sunansa.
Har yanzu shari’ar na ci gaba da gudana a kotun.