Masu garkuwa da mutane sun sace DPO – Daily Nigerian

0
15

An yi garkuwa da jami’in ‘yan sanda na DPO na sashen ‘yan sanda na Fugar, CSP Ibrahim Aliyu Ishaq a kusa da kogin Ise daura da tsohon titin Auchi-Ekperi-Agenebode a jihar Edo.

PRNigeria ta tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan dan sandan domin biyan kudin fansa.

Mista Ishaq kafin a tura shi aiki shekaru da suka gabata, ya taba rike mukamin DPO a sashin ‘yan sanda na Dakata a jihar Kano.

Cikakkun bayanai daga baya…

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=28463