Kanun Labarai
Manchester City na sha’awar sayen dan kasar Uruguay mai shekaru 20?
Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta nuna sha’awarta na daukar dan wasan bayan Montevideo City Torque Renzo Orihuela.
Alakar City da kungiyoyin kasashen waje ya ba su damar daukar matasa hazikai, tare da fatan shigar da su cikin tawagar farko.
An fahimci Orihuela ya dauki hankalin Man City, dan wasan mai shekaru 20 ya kafa kansa a matsayin dan wasa na farko tare da Torque bayan aro da kulob din Nacional ya yi.
A cewar kafar yada labarai ta Uruguay Referi, zakarun gasar Premier suna da wata magana a kwantiragin matashin na sayen dan wasan tsakiya, idan ya koma filin wasa na Etihad.
Orihuela ya buga wa Torque wasanni bakwai a kakar bana.