Kanun Labarai
limamin Katolika da aka sace ya samu ‘yanci
Cocin Katolika na Kafanchan jihar Kaduna, ta tabbatar da sakin Rabaran Fr. Emmanuel Silas, bayan sa’o’i 24 da wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da shi.
An yi garkuwa da Mista Silas ne daga dakin taro na cocin St. Charles Catholic Church da ke Zambina a karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna da sanyin safiyar ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Rev. Fr. Emmanuel Okolo, ya godewa duk wanda ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa.
“Da zukata masu cike da farin ciki, muna ɗaga muryarmu cikin kaɗe-kaɗe na yabo yayin da muke shelar dawowar ɗan’uwanmu, Rev. Fr. Emmanuel Sila.
“Masu dauke da makamai ne suka sace shi daga reshen cocin St. Charles Catholic Church, Zambina, a karamar hukumar Kauru, a safiyar ranar Litinin, 4 ga watan Yuli, 2022,” in ji sanarwar.
NAN