LABARI: An kashe fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Dogo Gide

0
36

PRNigeria ta ruwaito an kawar da wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Dogo Gide.

A watan Maris din 2018 ne Mista Gide ya kashe fitaccen dan fashin nan na wancan lokacin, Buharin Daji, inda ya zama sarkin yankinsa.

Kamar yadda ya kashe Mista Buharin Daji, wata majiya ta shaida wa PRNigeria cewa mataimakin shugaban kungiyarsa, Sani Dan Makama ne ya harbe Mista Gide ranar Lahadi.

‘Yan ta’addan da aka kashe sun dade suna addabar al’ummomi da dama a jihohin Zamfara, Neja, Kaduna, Katsina da Kebbi, tsawon shekaru.

“Laftanarsa mai suna Sani Dan Makama ne ya kashe Dogo Gide bayan wata ‘yar karamar rikici da ta barke a dajin Kuyanbana da ke hade Zamfara – Birnin Gwari – Dogon Dawa,” inji majiyar.

PRNigeria

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=26648