KU KARANTA: Buhari ya dawo Abuja

0
7

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yammacin ranar Talata ya dawo babban birnin tarayya Abuja, bayan shafe kwanaki 16 yana gudanar da aikinsa a kasashen Turai da Afirka ta Kudu.

Shugaban wanda ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 4:45 na yamma, ya taso ne daga birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, inda ya halarci bikin baje kolin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka karo na biyu na 2021.

Shugaban ya ziyarci kasar Afirka ta Kudu a ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba.

Kafin ziyarar Afirka ta Kudu, ya halarci taron zaman lafiya na Paris, PPF, a Faransa, inda ya isa a ranar Asabar, 9 ga watan Nuwamba, da farko a matsayin bakon shugaban Faransa, Emmanuel Macron.

Shugaba Buhari dai ya kasance a birnin Glasgow na kasar Scotland, kafin a tafi kasar Faransa, inda ya halarci taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya karo na 26, COP26.

Ya bar Najeriya zuwa Glasgow a ranar Lahadi, 31 ga Oktoba, 2021. Baki daya, al’amuran sun hana shugaban kasar barin kasar na tsawon kwanaki 16, bayan da ya tafi a ranar karshe ta Oktoba.

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=27750