Jiragen saman soji sun kashe mayakan ISWAP a madatsar ruwa da ke Kukawa

0
3

Sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan tada kayar baya da dama a wani gagarumin farmaki da suka kai a kusa da madatsar ruwan kifi a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PRNigeria cewa, an aiwatar da hare-haren ne a ranar Laraba bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne suka kai hari a sansanin soji da manyan motocin yaki guda goma sha biyu.

A yayin da sojojin kasa ke ci gaba da artabu da ‘yan ta’addan da aka kwashe sama da sa’a guda ana gwabzawa, jami’an rundunar sojin sama, ATF suka kai farmaki wurin.

Wani jami’in leken asiri ya shaidawa PRNigeria cewa jiragen yakin rundunar sun yi ruwan bama-bamai a kan ‘yan ta’addar, inda suka kawar da da dama daga cikinsu.

“Akwai wani rahoto da ya gabata wanda ke nuni da haduwar ‘yan ta’addan a kusa da dajin Duguri. Da alama suna shirin kai hari a kan sojojinmu da ke kusa.

“Duk da haka, sojojin da aka shirya musu, sun kama su. Sun kashe wasu daga cikinsu kafin sojojin sama su zo suka taimaka mana wajen tura da yawa daga cikinsu zuwa kakanninsu,” in ji jami’in.

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=27415