Hukumar NSCDC ta musanta zargin shigar da ‘yan ta’adda a Kano

0
3

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC reshen jihar Kano, ta yi watsi da wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa ‘yan bindiga daga jihohin Zamfara da Katsina na komawa jihar Kano.

Rahoton da ake zargin ya nuna cewa ‘yan bindigar da suka tsere daga farmakin jami’an tsaro, ana kyautata zaton sun kutsa cikin jihar Kano ta wasu al’ummomi a kananan hukumomin Shanono, Gwarzo da Kabo na jihar, inda a nan suke aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSC Ibrahim Idris-Abdullahi, ya fitar a Kano ranar Litinin.

Ya ce: “An tabbatar da bayanan da ke sama ba gaskiya ba ne”.

“A ranar 28 ga Oktoba, da misalin karfe 9:00 na safe, an ga wasu mutane a kan babura suna tafiya daga kauyen Danguzuri da ke karamar hukumar Makarfi a jihar Kaduna.

“Sun bi ta kauyen Zarewa da ke Jihar Kano, a kan hanyar Beli zuwa Babbarika, zuwa wani kauye na wani Shehu Danfulani, domin halartar wani bikin aure da nada suna a unguwar.

“Bayan an yi bikin, duk sun koma inda suka fito,” in ji shi.

Mista Idris-Abdullahi ya lura cewa Hakimin Kauyen Zarewa da Shehu Danfulani duk sun yi hira da jami’an tsaro kuma sun tabbatar da lamarin.

“Daga binciken da muka yi ya zuwa yanzu, babu ‘yan bindiga da suka koma kananan hukumomin Gwarzo, Kabo da Shanono, da kuma dajin Dansoshiya.

Sai dai ya ce rundunar tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro za su ci gaba da kara sanya ido domin kaucewa duk wani abin da ba a so.

NAN

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=26666