Connect with us

Kanun Labarai

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da raba kayan aikin gona ga manoma 7,386 na Borno

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon kayan aikin gona ga manoma 7,386 da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno a shekarar 2020.

A wata sanarwa da Abdulkadir Ibrahim, jami’in watsa labarai, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ofishin shiyyar arewa maso gabas, ya ce babban daraktan hukumar ta NEMA, Mustafa Ahmed ne ya yi rabon.

“Alhaji Mustapha Ahmed ya ce an zabo manoman ne daga kananan hukumomi 11 na jihar.

“Babban daraktan ya ci gaba da cewa rabon kayan aikin yana cikin cika shirin gwamnatin tarayya na farfado da manoma.

Sanarwar da aka nakalto ta ce “Zai bunkasa yawan aiki da kuma tabbatar da wadatar abinci.”

Ya bayyana cewa yayin da yake a Maiduguri, babban daraktan ya ziyarci Gwamna Babagana Zulum inda ya yabawa gwamnan bisa jajircewarsa na dawo da zaman lafiya da magance matsalar jin kai a jihar.

Sanarwar ta ruwaito cewa, Zulum a nasa bangaren ya godewa Gwamnatin Tarayya kan irin tallafin da take baiwa Borno.

“Babban Daraktan ya kuma yi wani taro da ma’aikatan ofishin shiyyar NEMA na shiyyar Arewa maso Gabas inda ya yaba wa ma’aikatan saboda sadaukar da kai ga aiki,” in ji shi.

NAN